KARKASUWAR MUTANE A HARKAR DIGITAL SKILLS
Mutane sun kasu kashi-kashi a harkar digital skills. Wasu sun yi nisa ƙwarai da gaske har sun kai matsayin su ne ke ƙirƙiro duk wata harka ta intanet. Wasu kuwa sam ko buɗe account na facebook ba su iya ba. Wasu suna matakin tsaka-tsakiya. Haka dai mutane suke daban-daban.
Mun san waɗanda suka yi zurfi ba su buƙatar wannan rubutun balle su tambayi ma menene Digital Skills. Waɗanda zasu yi wannan tambayar su ne waɗanda ba su san inda aka sa gaba a harkar ba. To mu kuma don su muka yi wannan rubutun.
Digital Skill shi ne duk wata iyawa ko ƙwarewa ko gogewa a harkar yanar gizo ta hanyar amfani da waya ko kwamfuta ko kuma duk wani kayan aiki da ke amfani da intanet.
Wannan skill kan iya zama na dole wato wanda wajibi ne mutum ya yi amfani da shi a wannan zamani musamman ma matasa. Wanda muke cewa survival digital skill. Ya kan iya zama kuma na son ƙwarewa ko kuma zama masanin wani fanni don gina career da yin sana'a ko kasuwanci. Wannan kuma shi ne Professional Digital Skill.
Kamar dai yadda muka sani yanzu zamani ne na intanet. Ta shiga komai na rayuwarmu gaba da baya. In ba mu yi amfani da ita ta wannan hanyar ba zamu yi ta waccan hanyar. Ke nan neman ilimi a kanta shi ma ya zama dole. Domin ba zaka haÉ—a wanda ya koyi ilimin amfani da Facebook ba da wanda yake yi da kundin kansa kawai. Dole za'a samu bambanci.
Sannan ba zaka haɗa wanda ya koyi yadda ake tallata kasuwanci a social media da wanda bai yi ba. Koda kuwa dukkaninsu suna yin tallar ka'in da na'in. Ko kuma ma a ce mara ilimin ya fi mai ilimin ƙoƙarin yin talla. To zai kasance tallar mai ilimi 1 zata yi daidai da tallar mara ilimi 100 ko fiye. Mai yiwuwa ne ma mara ilimin ya sare ya watsar saboda rashin samun biyan buƙata.
Haka zalika ba zaka haɗa mai ƙirƙiro shafukan AI da wanda yake amfani da su ba balle kuma wanda bai san yadda zai yi amfani da su ba. Nan ma dole a samu bambanci.
Bugu da ƙari da wanda yake da ilimin cyrptocurrency da wanda iyakarsa yin mining dole ne za'a samu bambanci. Duk yadda mai mining zai samu babu yadda za'a yi ya kamo mai cikakken ilimi. Domin shi dai bai wuce ɗan ƙwadago ba. Ka san kuwa ba shi yiwuwa ɗan ƙwadago ya fi Alhajin da yake yiwa aiki a gona samun amfanin gonar. Don gonar ba ta shi ce ba.
A taƙaice dai da mai ilimi a harkar digital skills da mara ilimi akwai bambanci sosai. Koda kuwa mara ilimin nan ya samu wata dama da yake ganin yana samun na kashewa fiye da mai ilimin a farkon al'amari. Idan da juriya mai ilimin sai ya ba wa mara ilimin tallafi wata rana.
Mu dawo kan maganarmu ta farko. Wato KARKASUWAR MUTANE A HARKAR DIGITAL SKILLS. A matsayinka na yadda kake ɗin nan ya kamata ka san a wane matsayin kake. Shin ka san wani abu a kai? Idan ka sani a ina ka tsaya? Wa ka fi wa ya fi ka? Idan ka yi zurfi, to Waɗanne abubuwa ne ka ƙirƙiro waɗanda dole a danganta asalinsu zuwa gare ka?
In kuwa ba ka san komai a kai ba to ta ina zaka fara? Su wanene zaka rinƙa bibiya don ka samu ka gane inda aka dosa?
Domin idan ka ce kowa zaka bi zaka ruɗe ne. Misali kai da ko email ba ka iya buɗewa ba ta ya ya zaka bi mai magana a kan yadda ake amfani da AI? Me zaka gane a nan? Balle kuma ka bi wanda yake ƙirƙiro AI ɗin. Ke nan kai ko firamare ba ka yi ba ka faɗa a JAMI'A. Anya zaka gama ta kuwa?
Saboda haka ka yi nazari ka san matsayinka. Social media ta tara kowa da kowa. Da mai zurfin ilimi da mai sama sama da kuma ɗif. Kuma kowa yana bayar da abin da yake da shi ne. To ka san wa zaka bi wanda zai amfane ka. Idan ilimin da mutum yake bazawa ya fi ƙarfinka babu dole ka bi shi. Ka bi wanda zaka iya fahimta da ganewa. Ta haka ne zaka kai matsayin da kai ma ba ka yi tsammani ba.
Idan ka san kana cikin waÉ—anda ko email ba su iya buÉ—ewa ba to ya kamata ka bibiyi Arewa Readers Technology. Aikinmu kenan. Karatun litattafai da zasu taimaka maka da kuma É—ora ka a kan hanya har kai ma ka san wani abu ka kai matsayin da zaka shiga makaranta irinsu FLOWDIARY a dama da kai.
Amma muna tabbatar maka cewa in ka tsallake Matakan farko a Digital Skills to ba zaka kai labari ba. Kamar wanda bai yi firamare ba ne ya ce zai shiga JAMI'A ne.
#digitalskills #Hausa #SmarphoneAwareness #BasicDigitalSkills #ArewaReadersTechnology
Telegram
https://t.me/arewareaderstechnology
https://chat.whatsapp.com/Fdd4HS92E4TJfWRmRFtkBm
https://www.facebook.com/share/15ygFVwsUX/
Arewa Readers Technology
Arewareaderstechnology@gmail.com
0 Comments
Mun Gode da Martanin ku!
Ku Karance tare da Arewa Readers Technology