Arewa Readers Technology na ƙoƙarin wayar da kan mutanen da ba su san inda aka sa gaba ba a harkar digital skills ko kuma ma kacokan amfani da wayar. Zaka samu mutane da yawa suna riƙe waya ta dubunnan ɗaruruwan kuɗi amma daidai da Security na wayarsu ba zasu iya sa wa ko su cire da kansu ba. To ina ga amfani da wasu abubuwa masu zurfi?
A wannan zamani da muke rayuwa amfani da Smartphones ya zama kamar dole. Yanzu ba za ka haɗa wanda yake amfani da keypad da kuma wanda yake yi da android ta fuskar mu'amala ta banki da account ba. Mai amfani da Smartphone ya fi samun sauƙi sosai fiye da wanda yake amfani da keypad. Ko wajen yawan cajis ma da sauran abubuwa mai smartphone ya fi samun sauƙi. Kai akwai wasu wallet ɗin ma sam ba zaka iya amfani da su da keypad ba.
Ta fuskar amfani da intanet da social media kuwa ai abun ba a cewa komai. Mai amfani da smartphone shi ke samun wannan garaɓasa da romuwa na intanet. Komai zaka same shi a sauƙaƙe. Duk abin da kake nema zaka samu.
Idan kuwa aka zo maganar neman aiki ko cike wani online form ko program ko neman wani bashi ko tallafi, to mai amfani da smartphone ba sai ya je cafe ba. Shi gmda kan shi zai yi waɗannan abubuwan a ɗakinsa a lokacin da yake so. Ba ruwansa da kashe kuɗi da kuma ɓata lokacinsa.
To amma a waɗannan abubuwan ko dukkan mutanen da ke amfani da babbar waya sun sansu? Akwai fa waɗanda in ba kallon fina-finai da kwamedi ba babu wani amfani da take masu. Suna da ita zasu bayar da kuɗi a buɗe masu email ko a duba masu saƙon da aka turo masu. Ko kuma a cike masu wani form ne neman aiki ko rijista ta makaranta. Abin mamaki har ka ga layi ya yi yawa a cafe. Alhali kuma a kullum sai sun sa data sun shiga YouTube ko Tiktok ko Facebook don kallon bidiyo kawai.
In kuwa aka taɓo ɓangaren amfani da social media ma karan kansa nan ma sai ka ga an bar wasu mutanen da yawa a baya. Wasu na da manyan wayoyi amma ba zasu iya buɗe social media accounts nasu da kansu ba. To ina ga aiki da shi da kiyaye shi tsawon lokaci?
Wasu kuma zasu iya buɗewa amma akwai gyare-gyare da yawa sannan ba zasu iya kula da waɗannan accounts ba. Har sai ma su ɗauka cewa kamar wani abin ƙwazo su buɗe wani yau a gobe kuma su sake buɗe wani daban. Saboda sun iya buɗewa ne kuma kawai babban dalilinsu na yin haka.
Kai a taƙaice dai akwai mutane masu ɗimbin yawa da suke buƙatar su samu jagoranci wajen abin da ya shafi BASIC DIGITAL SKILLS. Kai wasu ma sun yi nisa a PROFESSIONAL DIGITAL SKILLS har sun fara samun kuɗi da su amma suna da buƙatar waɗannan basic digital skills. Rashin shi kan rage masu abubuwan cigaba da yawa.
Wani lokaci ma hakan kan sa wani ya É—auki wani kwas É—in da bai dace da shi ba ko kuma wanda ba zai ba. Ko kuma ya rage ma shi saurin fahimta.
Ganin dai irin wannan buƙata da ke akwai ya sa Arewa Readers Technology ta zo don yin iya bakin ƙoƙarin ta kawo sauƙi da fahimtar da waɗanda ba su san ma menene digital skills ba.
Domin kasancewa da Arewa Readers Technology ku yi following É—in mu a social media handles namu.
https://www.facebook.com/profile.php?id=61563055777834&mibextid=ZbWKwL
Telegram Channel
https://t.me/arewareaderstechnology
WhatsApp Group
https://chat.whatsapp.com/Fdd4HS92E4TJfWRmRFtkBm

0 Comments
Mun Gode da Martanin ku!
Ku Karance tare da Arewa Readers Technology