KADA RASHIN REACTION YA KASHE MAKA ƘWARIN GWIWA


 


KADA RASHIN REACTION YA KASHE MAKA ƘWARIN GWIWA

Reaction a social media shi ne like da comment da sharing da sauransu kamar aikawa da emojis da sticker da kuma sauran alamomi. Samun waɗannan abubuwan kan sa mutum ya fahimci cewa ana amfanuwa da CONTENTS nasa. Kuma wannan ke nuna suna isa ga audiences nasa. Sannan kuma su ne dalilan da zasu sa profile ko page na shi ya tumbatsa. A taƙaice dai su ne burin kowa da kowa.

TO MENENE ILLAR RASHIN SAMUN REACTION?

Illa ta farko da rashin samun reaction yake da ita ita ce karya ƙwarin gwiwa musamman ga sabon Content Creator. Saboda bai sani ba shin Contents nasa suna samun karɓuwa ga mutane ko kuwa ba su samu. Menene ya kamata ya gyara? Wane irin Content ya fi jan hankali? Da dai sauran abubuwan da reaction ke taimaka wa content creator. Wannan sai ya sa ya rinƙa jin cewa kamar a banza yake yi. Ba a amfanuwa da abinda yake yi. In talla ya yi ba za'a ko taya ba. Idan wani link ya saka babu mai bi. Kawai sai ya fara tunanin dainawa in ba yana da passion da internal reinforcement ba.

Illa ta biyu kuma ita ce ba zai samu cigaba da wuri ba. Saboda wannan reaction shi ne ke taimakawa contents naka su je wurin da ba ka tsammani. Wani ma da wannan yake auna irin yarda da zai nuna maka. Kai wani ma idan ya ga babu like ko comment a post naka sai ya tsallake shi duk muhimmancinsa. To a haka ta ya ya zaka samu cigaba?

Illa ta uku kuwa ita ce rashin samun gyara da ƙarfafawa gwiwa da samun biyan buƙatunka da wuri. Kowa yana son idan ya yi ba daidai ba a gyara masa ta hanyar da ta dace. Sai dai mai girman kai ne kawai bai so. Saboda wannan gyaran da zai yi shi zai ɗora shi a kan daidai kuma ya samu ci gaba. Ka ga in babu mai gyara masa zai cigaba da zama cikin kuskure ke nan har sai lokacin da ya gano da kansa. Sannan kowa na son in ya nemi a yi wani abu a ce akwai mai yi ko mutum ɗaya ne. Wani yana buƙatar post naka amma ba shi da hanyar da zai gan shi sai ta hanyar sharing daga wani. Ka ga idan ba a samu wanda ya yi ba ba zai gani ba. To a haka ka ga kana rasa abubuwa da yawa.

TO TUNDA REACTION NA DA MUHIMMANCI HAKA TA YAYA ZAN RINƘA SAMUNSA?

A nan kana buƙatar fahimtar wasu abubuwa kamar haka :
1 IREN-IREN CONTENTS
Contents su ne rubutu da hotuna da bidiyoyi da alamomi da sauransu waɗanda ake ƙirƙira ake kuma yaɗawa a kafofin sadarwa na zamani. Wasu ana ƙirƙiro su don barkwanci wasu don koyarwa, ilimantarwa da wayar da kai. Wasu don nishaɗi wasu kuma don gargaɗi da nusarwa. 

Sannan wasu contents ɗin gajeru ne wasu kuma dogaye. Wasu suna buƙatar a kullum ka ɗora su wasu kuma koda sau ɗaya ne a sati ko a wata sun wadatar. Wasu na zuwa da siffar tambaya don neman amsa. Wasu kuma su zo da sigar bayar da labari. Kai wasu ma don motsa zuciya kawai ake ɗora su. Da dai sauran iren-ire da siffofi na contents. 

Sanin wannan zai ba ka damar sanin irin waɗanda ke jawo hankali da saurin sa mutane su yi reaction. 

2 IRE-IREN AUDIENCES/USERS
Audiences ko Users kuma su ne masu amfani da contents naka. Sanin mutane da halayensu yana da matuƙar tasiri wajen kawo reaction. Sannan shi ne zai sa ka yi contents naka waɗanda zasu kawo maka reaction. 
Misali Idan kai malami ne ba zai yiwu ka shiga groups na masu yin batsa ba ka ce zaka hana su ta hanyar wa'azi. Idan ka yi haka ba zaka samu biyan buƙata ba in ba cin mutunci ba. Tambaya ta farko da zasu fara yi maka shi ne idan ba ka so menene ya kai ka cikinsu? 

Sannan ba zai yiwu kana magana da Hausawa ba ka rinƙa yi masu magana da Turanci ko Larabci da nufin su fahimci saƙon har su yi reaction. Musamman kuma a ce mutanen da kake yi wa magana ma ba su je makaranta ba sai dai yaƙi da jahilci da suka yi. 

Sannan a mutane akwai wanda ya fi ka ilimi amma yana ƙaruwa da contents naka. Irin waɗannan yana da wahala su yi maka reaction. Saboda suna ganin kada su yi maka ka ce ai tun da akwai irinsu babu buƙatar ka rinƙa yi. Saboda sun fi ka ilimi kana iya bari. Kuma ba su so ka gane suna ƙaruwa da kai. Mai yiwuwa ne in ka bari ka ji suna cewa ai ya kamata ka ci gaba ai mutane na ƙaruwa. 

Sannan akwai waɗanda abin da kake posting ya fi ƙarfin ƙwaƙwalwarsu ko kuma ba su da sha'awarsa. Suma irin waɗannan ba kasafai suke cewa wani abu ba. 

Akwai waɗanda in dai ba abu na gardama da jayayya da musu da muhawara ba ne ba su iya yin reaction. Akwai mutanen da in abin ya kasance ba wanda za'a ce "amin" ba ne ba zasu iya cewa komai ba. 

Haka zalika wasu in ba tambaya ka yi ba sai dai su ƙura maka ido. Da yawa kuma wasu in ba da Allah da Annabi ka haɗa su ba to kai ba ka isa su yi maka reaction ba. Amma duk rashin muhimmancin abu in dai ka ambaci Annabi Sallallahu alaihi Wasallam sai sun yi reaction. 

To ga tafiya ta tafi amma ba mu kawo yadda zaka samu reaction ba da kuma babban batun da muka ɗauko. 

Zamu tsaya a nan sai a rubutu na gaba zamu cigaba. 

Ibrahim Musa Gozawa 
The Producer of Hausa Audiobooks 



Post a Comment

0 Comments