SANIN SIRRIN WAYA DA MUHIMMANCINTA GARE MU ABU NE DA YA ZAMA WAJIBI A WANNAN ZAMANI


 Arewa Readers Technology na Æ™oÆ™arin wayar da kan mutanen da ba su san inda aka sa gaba ba a harkar digital skills ko kuma ma kacokan amfani da wayar. Zaka samu mutane da yawa suna riÆ™e waya ta dubunnan É—aruruwan kuÉ—i amma daidai da Security na wayarsu ba zasu iya sa wa ko su cire da kansu ba. To ina ga amfani da wasu abubuwa masu zurfi? 

A wannan zamani da muke rayuwa amfani da Smartphones ya zama kamar dole. Yanzu ba za ka haÉ—a wanda yake amfani da keypad da kuma wanda yake yi da android ta fuskar mu'amala ta banki da account ba. Mai amfani da Smartphone ya fi samun sauÆ™i sosai fiye da wanda yake amfani da keypad. Ko wajen yawan cajis ma da sauran abubuwa mai smartphone ya fi samun sauÆ™i. Kai akwai wasu wallet É—in ma sam ba zaka iya amfani da su da keypad ba. 

Ta fuskar amfani da intanet da social media kuwa ai abun ba a cewa komai. Mai amfani da smartphone shi ke samun wannan garaɓasa da romuwa na intanet. Komai zaka same shi a sauƙaƙe. Duk abin da kake nema zaka samu.


Idan kuwa aka zo maganar neman aiki ko cike wani online form ko program ko neman wani bashi ko tallafi, to mai amfani da smartphone ba sai ya je cafe ba. Shi gmda kan shi zai yi waÉ—annan abubuwan a É—akinsa a lokacin da yake so. Ba ruwansa da kashe kuÉ—i da kuma É“ata lokacinsa. 


To amma a waÉ—annan abubuwan ko dukkan mutanen da ke amfani da babbar waya sun sansu? Akwai fa waÉ—anda in ba kallon fina-finai da kwamedi ba babu wani amfani da take masu. Suna da ita zasu bayar da kuÉ—i a buÉ—e masu email ko a duba masu saÆ™on da aka turo masu. Ko kuma a cike masu wani form ne neman aiki ko rijista ta makaranta. Abin mamaki har ka ga layi ya yi yawa a cafe. Alhali kuma a kullum sai sun sa data sun shiga YouTube ko Tiktok ko Facebook don kallon bidiyo kawai. 


In kuwa aka taÉ“o É“angaren amfani da social media ma karan kansa nan ma sai ka ga an bar wasu mutanen da yawa a baya. Wasu na da manyan wayoyi amma ba zasu iya buÉ—e social media accounts nasu da kansu ba. To ina ga aiki da shi da kiyaye shi tsawon lokaci? 


Wasu kuma zasu iya buÉ—ewa amma akwai gyare-gyare da yawa sannan ba zasu iya kula da waÉ—annan accounts ba. Har sai ma su É—auka cewa kamar wani abin Æ™wazo su buÉ—e wani yau a gobe kuma su sake buÉ—e wani daban. Saboda sun iya buÉ—ewa ne kuma kawai babban dalilinsu na yin haka. 


Kai a taÆ™aice dai akwai mutane masu É—imbin yawa da suke buÆ™atar su samu jagoranci wajen abin da ya shafi BASIC DIGITAL SKILLS. Kai wasu ma sun yi nisa a PROFESSIONAL DIGITAL SKILLS har sun fara samun kuÉ—i da su amma suna da buÆ™atar waÉ—annan basic digital skills. Rashin shi kan rage masu abubuwan cigaba da yawa. 


Wani lokaci ma hakan kan sa wani ya É—auki wani kwas É—in da bai dace da shi ba ko kuma wanda ba zai ba. Ko kuma ya rage ma shi saurin fahimta. 


Ganin dai irin wannan buÆ™ata da ke akwai ya sa Arewa Readers Technology ta zo don yin iya bakin Æ™oÆ™arin ta kawo sauÆ™i da fahimtar da waÉ—anda ba su san ma menene digital skills ba. 


Domin kasancewa da Arewa Readers Technology ku yi following É—in mu a social media handles namu. 


Facebook 

https://www.facebook.com/profile.php?id=61563055777834&mibextid=ZbWKwL


Telegram Channel 

https://t.me/arewareaderstechnology


WhatsApp Group 

https://chat.whatsapp.com/Fdd4HS92E4TJfWRmRFtkBm




Post a Comment

0 Comments